Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar kula da sufurin Jiragen Sama ta kasa (NCAA), Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar ranar Laraba, ta ce an dakatar da shi ne da nufin baiwa hukumar EFCC damar gudanar da bincike a kan sa da sauran manyan jami’an hukumar.

Karanta wannan:Gwamnatin tarayya ta cire Jami’o’I daga tsarin biyan albashi na IPPIS
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban kasar ya umarci Kyaftin Chris Najomo da ya fara aiki a matsayin mukaddashin shugaban hukumar nan take.













































