Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Lahadi ya kaddamar da aikin dashen itatuwa miliyan uku a fadin kananan hukumomin jihar 44 tare da hadin gwiwar hukumar Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACRESAL).
SOLACEBASE ta rahoto cewa kaddamar da shirin a wani taron biki, Gwamna Yusuf ya dasa bishiya a kan hanyar shiga gidan gwamnatin jihar.
Gwamnan ya ce atisayen zai kasance a manyan tituna a fadin kananan hukumomin jihar domin karfafa gwiwar mutanen jihar da su fito su fara dashen bishiyu a gidajensu, kan tituna da kuma dukkannin kananan hukumomin jihar.
A nasa jawabin, Ko’odinetan ACRESAL na Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya ce an gudanar da aikin ne domin kamo matsalar sauyin yanayi da ya jefa jihar ga matsanancin zafi na baya-bayan nan.