Tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya ta sake lalacewa karo na shida a cikin shekarar 2024.
Tashar ta samu matsala ne da misalin karfe 2.42 na safiyar yau, inda yanzu wutar da ake bayarwa ta fado zuwa megawatt 64.70 rak.
A bayanan da ISO dake samar da bayanai kan wutar lantarkin ya bayyana cewa kamfanin samar da wutar lantarki daya ne kacal, na Ibom Power ke aiki a yanzu.
Da yake tabbatar da lalacewar tashar, kamfanin samar da wutar lantarki a Jos ya ce: “Rashin wuta da ake samu a jihohin da muke ba wuta ya samo asali ne saboda rashin wautar daga tashar samar da wuta ta kasa. An samu katsewar samar da hasken wutar lantarkin a safiyar yau da misalain karfe 2.42, 15 ga watan Afrilu 2024, wanda ya haddasa rashin wuta ga dukkanin wuraren ajiyar wutar.”
Shugaban kamfanin, Dr. Friday Adakole Elijah ya bayyana fatan dawowar wutar domin su ci gaba da rarraba ta ga abokan hulda.