Majalisar ministocin Senegal ta amince da dokar yin afuwa ga fursunonin siyasa

Macky Sall, Senegal, majalisa, ministoci, amince, doka, fursunoni, siyasa, afuwa
Majalisar ministocin Senegal ta amince da dokar yin afuwa da nufin 'yantar da masu zanga-zanga da 'yan adawa da aka kama yayin zanga-zanga tsakanin shekarar...

Majalisar ministocin Senegal ta amince da dokar yin afuwa da nufin ‘yantar da masu zanga-zanga da ‘yan adawa da aka kama yayin zanga-zanga tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024, in ji shafin intanet na Dakaractu.

Shugaba Macky Sall ya buƙaci a gabatar da kudirin a gaban majalisar dokokin kasar.

Shugaba Sall bai bayar da karin bayani kan dokar da kuma yadda za ta iya shafar fitattun ‘yan adawar kasar ciki har da madugun ‘yan adawar kasar Ousmane Sonko da ke tsare a gidan yari a halin yanzu ba.

Karin labari: Amurka ta nuna damuwa kan dokar hana neman jinsi a Ghana

Rahoton ya ƙara da cewa Sall ya kuma buƙaci gwamnati da ta ba da taimako ga iyalan wadanda suka mutu a zanga-zangar da ta barke a baya-bayan nan.

A ranar 3 ga watan Fabrairu ne Sall ya ba da sanarwar ɗage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa tun a ranar 25 ga Fabrairu, shawarar da Majalisar Tsarin Mulki ta soke ranar 15 ga watan na Fabrairu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here