Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomin jihar su uku bisa zarginsu da almundahana. An bayyana sanarwar dakatarwar tasu a zaman majalisar na ranar Talata, 25 ga watan Yuli.
An zargi shugabannin ne da bayar da kwangiloli ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, kamar yadda dokokin jihar ta Kaduna suka tanada.
Kwamitin wucin gadi kan binciken wanda mamba mai wakiltar yankin Lere ta Gabas, Munirat Sulaiman Tanimu ta jagoranta, ya yi nazari sosai kan harkokin kuɗi na ƙananan hukumomin Chikun, Kaura, Kagarko, Soba, da Birnin Gwari.
Majalisar ce ta ba da umarnin gudanar da binciken, bayan wani ƙuduri da aka cimmawa a ranar 18 ga Yulin shekarar 2023.
Munirat ta ce sun nemi shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa, da su gabatar da bayanan duka kuɗaɗen da aka kashe a aika-aikace a ƙananan hukumomin nasu tun daga wata Yunin 2022 zuwa Yin 2023.
Ta ƙara da cewa bayan nazarin takardun ne suka gano cewa shugabannin Kaura, Kagarko, da Chikun sun sabawa sashe na 48 na dokar gudanar da ƙananan hukumomi na shekarar 2018, da sashe na 35 da ƙaramin sashe na 25 na dokar kadarorin gwamnatin jihar Kaduna na shekarar 2016.
Ta kuma ce waɗannan sassa sun zayyana yadda ya dace a kasafta kuɗi da kuma ka’idojin siyar da kayayyakin gwamnatin jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Sakamakon haka ne kwamitin ya ba da shawarar cewa, shugabannin uku su bar ofisoshinsu na tsawon watanni shida masu zuwa don ci gaba da bincike, sannan su miƙa ragamar shugabancin ga mataimakansu.
Gwamna Uba Sani dai ya sanar da naɗin sabbin shugabannin hukumomi, manyan masu ba da shawara na musamman da kuma hadiman da za su riƙa taimaka masa.










































