Kungiyar kwadago ta bawa gwamnatin tarayya sati daya data gyara wasu daga cikin tsare-tsaren data fitu dasu wadanda suka hada da tsadar man fetur ko kuma ta shiga yajin aiki daga ranar 2 ga watan Ogasta.
Kungiyar ta kuma umarci dukkan reshinan ta dake jihohin kasar nan da kuma Kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam dasu fara shirye-shiryen shiga yajin aiki mai tsayi wanda ya hada har da zanga-zanga idon har gwamnatin tarayya bata biya mata bukatun ta ba.
An tattaro rahoton cewa kwamatin koli na kungiyar ya cemma wanann matsayar ne a wani taro da ya yi a ranar 25 ga wannan watan da muke ciki a shalkwatar kungiyar dake Abuja