Yaren Hausa Da Yarbanci Na Cikin Harsuna 35 Da Za A Fassara Huɗubar Arfa Kai Tsaye A Bana

IMG 20260523 WA0183

Daga Aliyu Samba

Mahukuntan Ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa za a fassara huɗubar ranar Arfa ta Hajjin shekarar 2026 zuwa harsuna 35 na duniya, ciki har da Hausa da Yarbanci daga Najeriya, domin bai wa miliyoyin Musulmai damar sauraron saƙonnin huɗubar cikin yarukan da suka fi fahimta.

Shirin, wanda Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Masallacin Harami da Masallacin Annabi ﷺ ke jagoranta, zai kasance kai tsaye ta hanyoyin sadarwa na zamani da tashoshin yaɗa labarai masu alaƙa da aikin Hajji.

Hausa da Yarbanci na daga cikin jerin manyan harsunan da aka amince da su tare da Turanci, Faransanci, Indonesiya, Urdu, Turkanci, Farisanci, Sinanci, Rashanci, Hindi, Swahili da wasu da dama daga sassa daban-daban na duniya.

Mahukuntan Saudiyya sun ce manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa saƙonnin addini, nasiha da darussan da ke cikin huɗubar Arfa sun isa ga Musulmai a ko’ina cikin duniya ba tare da tangarɗar harshe ba.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Harami da Masallacin Annabi ﷺ, Abdulrahman Al-Sudais, ya bayyana cewa aikin fassarar huɗubar Arfa na daga cikin manyan shirye-shiryen da aka gina bisa gogewa da aka tara tsawon shekaru.

Ya ce shirin zai ba Musulman da ba sa jin Larabci damar amfana da saƙonnin ɗabi’a da jinƙai da huɗubar ke ɗauke da su, tare da isar da saƙon Musulunci na zaman lafiya ga duniya baki ɗaya.

Huɗubar Arfa, wadda ake gabatarwa a Dutsen Arafat a lokacin Hajji, na daga cikin mafi muhimmancin huɗubobi a Musulunci, kuma miliyoyin Musulmai a faɗin duniya na bibiyarta a kowace shekara.

A wani ɓangare kuma, mahukuntan Saudiyya sun sake tunatar da ƙasashen da ke halartar Hajji da su tabbatar da wayar da kan alhazansu kan bin ƙa’idojin aikin Hajji domin tabbatar da tsaro da nasarar gudanar da ibadar.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa tana ci gaba da daidaita ayyukanta da tsarin zamani, inda sashen fasahar sadarwa na hukumar ke aiki kan cikakken tsarin zamani domin inganta ayyukan Hajji daidai da hangen nesa na Saudiyya na shekarar 2030.

Masu lura da harkokin Hajji sun bayyana saka Hausa da Yarbanci cikin harsunan da za a fassara huɗubar Arfa a matsayin wani muhimmin mataki da ke nuna muhimmancin al’ummar Musulman Najeriya a duniya, tare da bai wa miliyoyin masu magana da waɗannan harsuna damar sauraron huɗubar kai tsaye cikin sauƙi da fahimta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here