Kakakin majalisar dokokin Ekiti ya rasu

Afuye
Afuye

Kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti Rt Hon. Funminiyi Afuye ya rasu.

Afuye wanda ke wakiltar mazabar Ikere ta 1, ya rasu ne a yammacin ranar Laraba yana da shekaru 66 bayan yasha fama da gajeruwar jinya.

Gwamnatin jihar ta ce shugaban majalisar ya rasu ne a asibitin koyarwa na jihar.

“Rt. Hon Afuye ya rasu ne da yammacin Laraba a asibitin koyarwa na jihar Ekiti, Ado-Ekiti, inda yake jinya bayan ya yi fama da ciwon bugun zuciya,”

Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Yinka Oyebode ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ayau Laraba.

Marigayi shugaban majalisar ya bayyana a wajen bikin rantsar da Gwamna Biodun Oyebanji, a ranar Lahadin da ta gabata, kuma an ce ya kuma halarci zaman majalisar a ranar Talata kafin aukuwar lamarin a ranar Laraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here