Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele, ya musanta zargin da ake masa na amincewa da buga Naira miliyan 684.5 kan kudi Naira biliyan 18.96.
Emefiele ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume hudu a gaban mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Karin labari: EFCC ta gurfanar da Emefiele a kotu bisa laifin buga takardun kudi
A tuhume-tuhume hudu da hukumar EFCC ta shigar a gabansa, ta yi zargin cewa Emefiele ya bijirewa umarnin doka da nufin yi wa jama’a rauni a lokacin da yake aiwatar da manufar musanya naira ta gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma zargi Emefiele da amincewa da cire Naira biliyan 124.8 ba bisa ka’ida ba daga asusun tara kudaden shiga na tarayya.
Cigaban labarin na nan tafe…