Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Godwin Emefiele, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN a gaban kuliya bisa wasu tuhume-tuhume guda hudu.
An gurfanar da tsohon gwamnan na CBN ne a gaban wata mai shari’a a wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayyar Abuja, Maryann Anenih, saidai ya musanta aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da shi.
Karin bayani: Kungiya Ta Yi Allah Wadai Da Mafi Karancin Albashin Ma’aikatan Jihar Borno
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa na zargin Emefiele da buga kudin Naira a sabon caji ba bisa ka’ida ba.
Cikakkun bayanin na nan tafe…