Majalisar wakilai ta gayyaci hukumar kashe gobara ta tarayya kan hatsarin motar da ya kashe mutane 3 a Abuja

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Majalisar Wakilai ta bai wa shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa (CG) Jaji Abdulganiyu wa’adin sa’o’i 24 da ya bayyana a gabanta, ya kuma yi bayanin abubuwan da suka faru a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon hadarin motar gobara da ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu a Abuja.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Ali Isah ya bayar da wa’adin ne a ranar Talata bayan da shugabannin hukumar suka kasa amsa gayyatar da aka yi musu a baya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ‘yan uwa uku, ya faru ne da yammacin ranar Juma’a a mahadar kungiyar ECOWAS da ke Wuse 2, Abuja, yayin wani aikin kashe gobara a Avenue Plaza, Banex.

Isah ya ce, majalisa ta ga bidiyon yadda lamarin ya faru amma bata ga wata sanarwa da hukumar ta fitar ba.

Dan majalisar ya umurci ma’aikatan da su gaggauta ziyartar ’yan uwan mamatan domin jajanta musu, da biyan kudaden jinya na wadanda ke asibitin tare da yin tanadin biyan diyya.

Ya ce, ya kamata hukumar ta sanya matakan da suka dace don ganin irin wannan lamari bai sake faruwa ba.

Karin karatu: NiMet ta ce za a fuskanci rana mai zafi da tsawa daga Laraba zuwa Juma’a 

Tun da farko, Mataimakin Kwanturola-Janar na gudanarwa da kula da harkokin kaya na hukumar, Samuel Olumode, ya ce hukumar ta yi nadamar faruwar lamarin.

Ya ce babu wanda zai so a rasa ko wace rai, musamman saboda babu wanda zai iya haifar da rai ko maye gurbinsa da zarar an rasa, yana mai dora alhakin faruwar lamarin a kan gaggawar aikin.

Ya bayyana cewa direban motar kashe gobarar da hatsarin ya rutsa da shi bai tsaya ba saboda fargabar gungun jama’a.

Sai dai mataimakin shugaban hukumar ya ce direban motar ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa kuma tun a lokacin yake tsare.

Olumode ya bayyana cewa hukumar karkashin jagorancin CG ta dauki matakai da dama da suka hada da ziyartar iyalan mamatan da kuma wadanda ke kwance a asibiti.

Ya ce tawagar jami’an kashe gobara sun kuma halarci jana’izar da aka yi a masallacin kasa.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here