Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya amunce da nada kakakin majalisar jihar Alhaji Nasiru Magary, a matsayin shugaban Alhazan jihar na bana.
Bayanin nadin na dauke cikin wata sanarwa da sakataran gwamnati jihar, Kabiru Balarabe ya sawa hannu a Gusau yau Litinin.
“Alhaji Farouk Musa Dosara, shugaban majalisar, Abubakar S-Pawa, kwamishina mai kula da harkukin kananan hukumomi, sarkin Talata-Mafara, Alhaji Bello Barmo; da kuma shugaban malaman jihar, Sheikh Ahmad Kanoma.
“Sauran ‘yan tauwagar sun hada da Babangida Abubakar-Anka, Musa Ibrahim-Yau, Hajiya Asiyatu Suleiman, sai kuma babban sakataran ma’ikatar kula da aiki da sifiri Garba wanda shine sakataren tawagar.” .