Shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar ya ce ‘yan boko haram sunyi garkuwa da mata biyu a kauyen Mairari da ke karamar hukumar Konduga.
Umar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa al’amarin ya faru 7 ga watan da muke ciki na shekarar 2022.
Ya kara da cewa yayin da hukumar ta samu labarin garkuwar, sun tura jami’an su domin su kubutar da wadan da abin ya rutsa dasu, amma hakan su bai cimma ruwa ba.
Inda ya tabbatar da cewa hukumar zata fadada binkice har sai ta kubutar da wadan da akayi garkuwar da su.
Ya kuma ja hankalin jama’a da su bada rahotan duk wani al’amarin da basu yarda da shiba a garuruwan su.













































