Hukumar Kula da Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano (AKTH) ta musanta zargin rashin da’a da ake yi wa likitan asibitin a shirin Berekete Family Arewa.
Wata sanarwa da babbar jami’ar yada labarai ta asibitin, Maryam Aminu Usman ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata, ta ce bisa ga binciken farko da asibitin ya gudanar, zargin da akewa likitan asibitin karya ne, amma asibitin zai kara yin bincike cikin gaggawa kuma bisa ka’idojin da aka tsara domin gano gaskiyar lamarin.
Jaridar SolaceBase ta tattaro cewa wata mata ta kasance a shirin Berekete Family Arewa a makon jiya inda ta yi zargin an cire mata mahaifa a AKTH ba tare da izininta ba a shekarar 2017.