Badakalar Dala Miliyan 52.8: Diezani Ta Tona Asirin Me Hannu Cikin Badakar Kudin

Diezani Alison Madueke

Tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta nisanta kanta da dala 52. 8m wadanda kwanan nan aka dawo da su Najeriya daga Amurka.

Sabanin wasu rahotannin da aka samu, tsohuwar ministar wadda ta bar Najeriya take zaune a kasar Ingila ta ce kudin ba nata ba ne.

A cikin wata sanarwa mai taken “Babu wani abu mai suna Diezani Loot, Alison-Madueke ta yi ikirarin cewa kudaden da ake alakanta ta da su, mallakin babban mai arzikin man Najeriya ne, wato Kola Aluko.

A cikin sanarwar da ta fitar ta hannun lauyanta, Farfesa Mike Ozekhome (SAN), tsohuwar ministar ta ce babu wani abu kamar “Diezani Loot.”

Da take bayyana yadda kudaden da aka wawashe suka shigo, Alison-Madueke ta ce Dala miliyan 52.8 sun fito ne daga wani jirgin ruwa da gwamnatin Amurka ta kwace daga hannun Aluko.

A cewarta, daga baya aka sayar da jirgin kuma aka mayar da kudaden da aka samu ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Da take bayyana rahotannin da ake alakanta ta da kudaden da aka dawo da su, acewar tsohuwar ministar wadanda suka yada wannan bayanin sunyi hakane don bata mata suna, ya kara da cewa ba ta-da hannu kwata kwata a saye ko amfani da jirgin ruwan da aka kama.

Yanzu sun kira shi “Babu wani abu makamancin haka da ya taɓa faruwa. Ba ta taɓa shiga cikin saye, amfani da siyar da jirgin ruwan da aka kama ba.

Don haka, ta shawarci masu yada bayanan da ba su da tushe, su yi kyakkyawan amfani da lokacinsu su bar ta ita kadai ta huta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here