Rahotanni daga kasar ingila sun ce wata kotu ta tabbatar da samun tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice, da laifin safarar sassan jiki a kasar Birtaniya.
Mutanen biyu tare da diyarsu, Sonia, da wani likita, Dokta Obinna Obeta, an same su da laifin taimaka wa wani matashin tafiya Biritaniya da nufin cirar sassan jikin sa, shari’ar da aka shafe makonni shida ana yi a Old Bailey.
Laifukan sun hada baki ne wajan kawo matashin dan kasuwa mai shekara 21 a Legas zuwa Landan domin amfani da kodarsa, kamar yadda alkalai suka gano a ranar Alhamis.
Jaridar Guardian UK ta rawaito mai shari’a Jeremy Johnson, zai yanke hukunci nan gaba kadan.
Idan za ku iya tuna cewa rundunar ‘yan sandan birnin Landan ta kama Ike Ekweremadu da matarsa tare da tsare su a watan Yunin 2022. An zarge su da hada baki wajen safarar wani mutum dake gararanba zuwa Burtaniya domin ya cirar kodarsa domin dasawa ‘yarsu.













































