‘Yan Majalisar Wakilai a Najeriya na dab da cirewa Jami’o’in Tarayya kudin wutar lantarki

'Yan Majalisar, Wakilai, Najeriya, dab da, cirewa, Jami'o'in, Tarayya, kudin, wutar, lantarki
Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta tabbatar da cewa an cire Jami’o’in Tarayya daga tsarin kudin wutar lantarki na Band A don rage makudan kudin wutar...

Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta tabbatar da cewa an cire Jami’o’in Tarayya daga tsarin kudin wutar lantarki na Band A don rage makudan kudin wutar lantarki.

Shugaban kwamitin majalisar kan ilimin jami’o’i, Abubakar Fulata, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja bayan zaman kwamitin da ke kula da jami’o’in tarayya na Arewa maso Gabas.

Wasu daga cikin jami’o’in gwamnatin tarayya da suka ziyarta a cewarsa, sun hada da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi da kuma Jami’ar Tarayya ta Kasa ta Jihar Gombe.

Ya ce ana kokarin cire jami’o’i da sauran manyan makarantu daga kungiyar masu amfani da wutar lantarki ta Band A.

Karin labari: “Ku bayyana Sunayenku da Adireshinku ga ‘Yan Sanda” – IGP Ya Fadawa Jagororin Shirya Zanga-zanga

Fulata ya ce ‘yan majalisar sun kuduri aniyar kawar da matsalolin da ke kawo cikas ga gudanar da makarantun cikin sauki.

Ya kuma bayyana fatansa na cewa gwamnati za ta saurare su sannan ta cire jami’o’i daga cikin shirin Band A na masu amfani da wutar lantarki kamar yadda suka yiwa IPPIS.

Kwamitin ya ce galibin jami’o’in na fuskantar wahalar biyan kudin wutar lantarki sakamakon karin kudin wutar lantarki.

Fulata ya kuma dora alhakin kula da jami’o’in biyu da su yi iya kokarinsu wajen bin dokokin da suka dace, musamman dokar kasafi.

Karin labari: Majalisar Wakilan Najeriya ta bawa shugaban Hukumar EFCC kwana 4 ya bayyana gabanta

Wakilin kwamitin, Victor Ogene, ya ja hankalin mahukuntan ATBU kan wasu alkaluma da ba a iya daidaita su ba dangane da kudaden shiga da kuma kudaden da makarantar ke kashewa tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.

Ya ce bai dace wata cibiya ta gwamnati ta kashe fiye da kudin shigarta wajen samar da kudaden shiga kamar Guest House ba.

Wani mamba, Adamu Gamawa, ya ce ba a yarda a kashe karin kasafin kudi ba saboda ya sabawa kundin tsarin mulki.

“Misali, ba za ka iya kasafta Naira miliyan 10 ka kashe Naira miliyan 15 ba. Shi ya sa ake samun karin kasafin kudin,” in ji Adamu.

Karin labari: An samu jikkatar wasu kananun yara dalilin fashewar Bam a Yobe

Farfesa Sani Kunya, mataimakin shugaban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya yabawa kwamitin tare da neman goyon bayan ‘yan majalisar domin tunkarar kalubalen da cibiyar ke fuskanta.

Hakazalika, Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya Kashare a jihar Gombe, Farfesa Umaru Pate, ya yabawa ‘yan majalisar bisa ziyarar da suka kai makarantar.

Pate ya ce baya ga kalubalen samar da ababen more rayuwa, galibin malamai ba sa son yin aiki a cibiyar saboda kalubalen tsaro kamar yadda NAN ta shaida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here