
Dakarun hadin gwiwa na Sashen II na Operation ‘Hadin Kai’ na Arewa maso Gabas a ranar Juma’a, sun dakile wata na’urar fashewa da aka dasa a Kasuwar Shanu ta Buni Yadi da ke Yobe.
Kaftin Mohammed Shehu, kakakin sashen ya shaidawa NAN a Damaturu cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bam din, inda suka auna ‘yan banga.
Sai dai ya ce wani bam da aka dasa a kasuwar ya fashe wanda ya raunata wani karamin yaro da ke sharar ruwan buhu.
Karin labari: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan bindiga 2 a Katsina
Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce yarinya ‘yar shekara 12 da haihuwa ta samu karaya a kafarta sakamakon fashewar.
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasa da su rika kai rahoton wadanda suka yi zargi ko wani abu zuwa ga jami’an tsaro domin daukar mataki.
Buni Yadi, na da tazarar kilomita 54 daga Damaturu, babban birnin jihar kamar yadda NAN ta wallafa.