Gwamnatin tarayya ta musanta rage alawus alawus din dalibai

Tahir Mamman 750x430

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da wani shiri na rage alawus alawus din dalibai kamar yadda aka yadawa kwanan nan a kafafen yada labarai.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a ya yin wata ganawa da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) a Abuja ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaitu cewa, ma’aikatar ta hannun hukumar ba da tallafin karatu na gwamnatin tarayya ta sanar da rage alawus alawus din daliban Najeriya da suke a kasashen waje, kamar daliban dake karatu a Rasha, Morocco, da Aljeriya da dai sauransu.

An danganta raguwar alawus din da tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.

Mamman ya ce, ba a samu raguwar alawus din dalibai ba sai dai an yi gyara ne saboda sauyin canjin kudaden waje (FOREX)

“Muna so mu fayyace abin da ke faruwa a kafafen yada labarai game da alawus-alawus da aka biya wa daliban dake karatu a kasashen waje karkashin yarjejeniyar bayar da tallafin karatu na kashi na biyu.

“Muna so mu sanar da al’umma cewa gwamnatin tarayya bata rage alawus din dalibai ba.”

“Amma a yanzu, abin da ke cikin kasafin kudin Najeriya shine abin da za mu iya biya.” inji shi.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here