‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan bindiga 2 a Katsina

'yan sanda, kama, wasu, ‘yan bindiga, Katsina
Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, ta ce ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da taimakawa ‘yan fashi da makami tare da kwato dabbobin da...

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, ta ce ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da taimakawa ‘yan fashi da makami tare da kwato dabbobin da ake zargi da satar su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Alhamis.

Ya ce an samu wannan nasarar ne a karamar hukumar Jibia, tare da hadin gwiwar kungiyar al’umma ta jiha (KSCWC) da mafarauta.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya daga likafar fanshon jami’an sojin ruwa

“A ranar 25 ga watan Yuli, 2024, tawagar ‘yan sanda da ke hedikwatar ‘yan sanda ta Jibia a yayin da suke sintiri na yau da kullum tare da hadin gwiwar KSCWC da mafarauta, sun yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi dukkansu ‘yan kauyen Zandam ne a karamar hukumar Jibia.

“An kama wadanda ake zargin ne a makabartar Magama dauke da raguna biyu da tunkiya daya, da kuma akuya daya, wadanda ake zargin sato su aka yi,” in ji shi.

Sadiq-Aliyu ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasarar ne sakamakon ci gaba da kokarin da rundunar ta keyi na yaki da ‘yan fashi da makami, karkashin jagorancin kwamishina Mista Aliyu Abubakar-Musa kamar yadda NAN ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here