Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Maryam Namadi Umar a ranar Laraba.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Hamisu Gumel ya fitar, ya tabbatar da cewa Hajiya Maryam Namadi Umar ta rasu a safiyar yau.
Rasuwar ta ta zo ne da matukar kaduwa, wanda ya zo daidai da ziyarar aiki da gwamnan ya kai kasar Sin, inda ya ke gudanar da kokarin bunkasa dangantakar tattalin arziki da jawo jarin jihar Jigawa.
Rashin zuwan gwamnan a yayin wannan babban rashi ya sanya shakku kan samun damar halartar jana’izar da aka shirya yi a yau.
Duk da kasancewarsa da nisa da gida, Gwamna Namadi ya nuna alhininsa tare da nuna jin dadinsa da ta’aziyyar da aka samu daga sassan jihar da ma sauran sassan jihar.