Wadanda suka sace tsohon shugaban NYSC sun bukaci Naira miliyan 250 kudin fansa

Marazi Tsiga

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da tsohon Darakta-Janar na Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, sun bukaci a biya shi Naira miliyan 250 kudin fansa domin su sake shi.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a ranar Asabar cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan mamacin a daren juma’a inda suka bukaci adadin kudin da suka ambata.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito cewa an yi garkuwa da Tsiga tare da wasu mazauna kauyen Tsiga dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, a ranar Laraba bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka mamaye gidan tsohon Darakta Janar na NYSC.

Karin labari: Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NYSC da wasu mutane a Katsina

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels afkuwar lamarin ta wata wayar tarho ranar Alhamis, wanda harin da ya dauki ‘yan mintuna, har ma wasu mazauna garin biyu suka samu raunuka, daya daga cikin ‘yan bindigar kuma ya mutu bayan da abokan aikinsa suka harbe shi cikin kuskure.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta tabbatar da yin garkuwa da Janar Tsiga mai ritaya, inda ta bayyana cewa suna kan bincike da sauran hukumomin tsaro a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar domin duba nasarorin da aka samu na yaki da miyagun laifuka a cikin watan Janairun 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here