Rashawa Ta Yi Katutu Zamanin Buhari – Bishop Kukah

1689068386805
1689068386805

Bishop na ɗariƙar Katolika a yankin Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya ce ba a taɓa cin rashawa a Najeriya kamar zamanin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Bishop Kukah ya bayyana haka ne ranar Litinin a jawabin da ya gabatar wurin bikin cikar Aare Afe Babalola SAN shekaru 60 da zama lauya.

Limamin cocin ya ce duk da dai ba a mulkin Buhari aka  fara cin rashawa a Najeriya ba, amma lamarin yafi muni a zamaninsa.

Ya ce ‘A waccan gwamanatin mun ga mafi nunin cin rashawa ta fannin tarbiyya, hada-hadar kuɗi, da ma fannoni da dama.’

Bishop Kukah ya kuma koka da yadda shugabannin suke tattare ayyukan ci gaban al’umma zuwa yankunan da suka fito.

Ya ce hakan ba zai taimaka wurin bunƙasa dimokraɗiyya a Najeriya ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here