Masu amfani da Thread sun kai miliyan 100 a kwana biyar

1689006588597
1689006588597

Mutane sama da million ɗari ne suka yi rajista da Threads, sabon manhajar sada zumunta da aka kaddamar kwanaki biyar da suka wuce.

Wanna yana nufin Threads, wanda kamfanin Meta ya ƙaddamar, ya buge tarihin da aka kafa manhajar AI’s ChatGPT ya kafa a baya.

An sabuwar manhajar akan dandalin manhajojin Apple da Android a cikin ƙasashe 100 a ranar Larabar da ta gabata.

Amma har yanzu manhajar ba ta kai Turai ba saboda rashin tabbas kan dokar sirrin bayanan EU.

Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, wanda kuma ya mallaki Facebook, ya ce manhajar ta samu rijistar mutane miliyan 10 a cikin sa’o’i bakwai da kaddamar da ita kuma sama da miliyan 30 a safiyar Alhamis.

Sa’o’i 24 bayan haka, adadin mutane da suka yi rajistar amfani da manhajar ya ninka fiye da sau biyu.

A mabiya miliyan 100, a alkaluma da dandalin bayanai na Quiver Quantitative ya fitar, Threads ya kasance yan kasa da kashi ɗaya cikin uku na yawan mutane da ke amfani da Twitter.

Wasu masu amfani da shafin Twitter sun nuna rashin jin daɗi tun lokacin da Elon Musk ya karɓi kamfanin.

An kori ma’aikata da dama tun bayan da Musk ya sayi shafin, inda kuma ya sanar da sauye-sauye don taimakawa wajen samar da kuɗaɗen shiga a Twitter.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here