Majalisar dokokin jihar jigawa ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomin guda uku

Jigawa map
Jigawa map

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku saboda rashin biyayya.

SOLACEBASE  ta rahoto cewa shugabannin da aka dakatar sun hada da Hon Mubarak Ahmed na karamar hukumar Birniwa, Hon Rufai Sunusi, karamar hukumar Gumel, da Hon Umar Baffa na kananan hukumomin Yankwashi.

Dakatarwar ta biyo bayan zargin cewa shugabannin sun je kasar Rwanda ne ba tare da neman izini daga bangaren zartarwa ko majalisar dokoki ba.

Majalisar ta dauki matakin ne bayan da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi Hon Aminu Zakari Tsubut ya gabatar da bukatar dakatar da shugabannin kansilolin da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here