Tsohon Ministan Kudi, Dr Onaolapo Soleye, ya rasu.
Wata sanarwa da iyalansa suka fitar a ranar Laraba ta ce tsohon ministan ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba, yana da shekaru 90 a duniya.
Soleye, wanda ya kasance ministan kudi a zamanin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya rasu kwanaki hudu kacal bayan ya yi bikin cika shekaru 90 a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.