Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu na Legas

Babajide Sanwoolu new 510x430
Babajide Sanwoolu new 510x430

Kotun ɗaukaka ƙara da ke jihar Legas ta tabbatar da nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu, a matsayin zaɓabɓen gwamnan jihar.

Alkalan kotun ɗaukaka ƙaran a wani mataki na bai ɗaya, sun yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar saboda rashin gamsassun hujjoji.

Mai shari’a Yargata Nimpa, da mai shari’a Samuel Bola da kuma mai shari’a Paul Bassey ne suka yanke hukuncin.

Ita ce shari’ar gwamna ta farko da kotun daukaka kara a Najeriya ta yanke, tun bayan zabukan watan Fabrairu na 2023.

Babajide Sanwo-Olu ya lashe zaɓen gwamnan Lagos ne a matakin wa’adi na biyu.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓe na jihar, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya ce Sanwo-Olu ya yi nasara da adadin ƙuri’a 762,134.

Yayin da jam’iyyar LP ta zo ta biyu inda ɗan takararta, Gbadébo Rhode-Vivour ya samu ƙuri’a 312,329, sai kuma ɗan takarar PDP Abdulazeez Olajide Adeniran da ya zo na uku da ƙuri’a 62,449.

Sai dai, har yanzu duk bangaren da bai amince ba, yana da dama ta karshe a shari’ance, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here