Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, tare da wasu manyan baki sun halarci jana’izar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi a wajen jana’izar da aka yi ranar Laraba.
Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II shi ma ya halarci taron.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Marigayi Galadima ya rasu ne a daren ranar Talata a gidansa da ke Kano, sakamakon doguwar jinya da ya yi, yana da shekaru 92 a duniya.
Karanta: Yanzu-yanzu: Galadiman Kano Abbas Sunusi ya rasu
Dubban jama’a ne suka halarci sallar jana’izar, wanda Farfesa Sani Zahradden ya gudanar a kofar Kudu, fadar Sarkin Kano.
An binne gawar Galadima a makabartar Gandun Albasa.
A matsayin girmamawa, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shagulgulanta na Sallah, yayin da Sarkin na 15, Aminu Ado Bayero, shi ma ya dakatar da harkokinsa na Sallah domin alhinin rasuwar Galadima.
Marigayi Galadima wanda ya rike mukami mafi girma a masarautar Kano, kuma shine mahaifin Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Kano.