Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin sai baba ta gani a kan abin da suka kira gazawar gwamnatin na magance matsalolinsu.
Yajin aikin likitoci a Najeriya na shafar ayyukan da ake yi a asibitoci musamman na gwamnati.
Daga cikin bukatun likitocin akwai biyansu dukkan albashinsu da kuma alawus alawus din da ya kamata a basu.
Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akalla likitoci 50 na barin ƙasar a kowanne mako inda suke fita kasashen waje don su yi aiki a can.
Rashin biyan likitoci albashi mai kyau da rashin cikakkun kayan aiki a asibitoci da ma tsadar rayuwa na daga cikin abubuwan da ke sa likitoci fita daga kasar don neman aiki a waje.