Dakatacciyar ministar harkokin jin kai Dakta Betta Edu, ta isa hedikwatar Hukumar EFCC, domin amsa tambayoyi bisa zargin almundahanar Naira miliyan 585 a ma’aikatar ta.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Tinubu ya dakatar da Betta Edu
Idan dai za’a iya tunawa dai a ranar Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Edu.
An zargi ministan da tura wasu kudade a wani asusu har Naira miliyan 585.
Wanda aka ce za’a yi amfani da shi ne don biyan tallafi ga marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Legas, Cross River da kuma Ogun.
Karanta wannan: Wani mutum ya mutu a Kano sakamakon kamawar wata Trailer da wuta
Edu dai ita ce minista ta farko da aka dakatar daga aiki tun bayan rantsar da mambobin majalisar zartarwa a watan Agustan shekarar da ta gabata.