Gwamnati ta dakatar da biyan mafi karancin Albashi-TUC

BREAKING 750x430
BREAKING 750x430

Kungiyar Kwadago TUC ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta daina biyan mafi karancin albashi na Naira 35,000 bayan wata daya duk da cewa tana da kudade.

Shugaban Kungiyar Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin.

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya Da Kungiyar Likitoci Masu Yajin Aiki Sun Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna

Ya ce gwamnati ta dakatar da biyan mafi karancin albashin na watanni 6 bayan an fara biya.

A halin da ake ciki kuma, TUC ta baiwa shugaban kasa Bola Tinubu wasu abubuwa 10 a matsayin wani bangare na bukatunta ga gwamnatin tarayya.

Karanta wannan: Kungiyar ƙwadago za ta shiga yajin aikin gargaɗi kan janye tallafin fetur

Osifo ya lura cewa gwamnati ba ta tantance batutuwan guda 10 da TUC ta gabatar mata ba, wanda a karshe aka amince da su.

Ya ce bukatun da TUC ta jera a cikin ajandodin guda 10 sun zo ne a daidai lokacin da talakawan Najeriya ke fama da wahalhalu sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, da cire tallafin man fetur, da sauran matsalolin tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here