Kungiyar ƙwadago za ta shiga yajin aikin gargaɗi kan janye tallafin fetur

NLC rivers
NLC rivers

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta sanar da anniyar shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu kan matsin da ‘yan ƙasar ke ciki sakamakon janye tallafin fetur.

NLC ta ce za ta gudanar da yajin aikin ne a ranakun Talata da Laraba mai zuwa.

A ranar da aka rantsar da shi, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man fetur, yanayin da ya haifar da tsadar man daga naira 197 zuwa naira 617.

NLC ta nuna ƙin amincewa da matakin gwamnati da aiwatar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu ya sha ganawa da ‘yan ƙwadagon a kokarin ganin an cimma daidaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here