UNGA: Shettima zai gabatar da jawabin kasa na Najeriya a yau Laraba

Kashim Shettima UNGA NEW 750x430

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, na shirin gabatar da jawabin kasa na Najeriya a yau Laraba a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) da ke gudana a birnin New York.

Shettima zai yi jawabin ne a madadin shugaban kasa Bola Tinubu tsakanin ƙarfe 3:00 na rana zuwa 9:00 na dare agogon kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Najeriya za ta bayyana sabbin bayanan ta na karkashin yarjejeniyar Paris a yayin jawabin.

A baya, Shettima ya halarci zaman bude taron, inda shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da muhimmin jawabi na maraba ga shugabannin duniya da suka halarta.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN kan muhimmancin jawabin Najeriya, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Stanley Nkwocha, ya ce sakon kasar zai karbu a matakin duniya.

Ya bayyana cewa tun bayan hawa mulki, Shugaba Tinubu ya sake fasalin jagoranci a Najeriya, yana jaddada diflomasiyyar ilimi, al’adu, wasanni, tsaro da tattalin arziki.

Ya kara da cewa a 2024, jawabin Tinubu a UNGA ya kasance mai ƙarfi, inda ya nemi a kara kujeru ga kasashen Afirka a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here