Haɗakar Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i da ba malamai ba (NASU) sun sanar da tsawaita wa’adin yajin aikin gargaɗi da suka bai wa gwamnati na tsawon makonni biyu.
Tun da farko, ƙungiyoyin biyu sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai kan matsalolin jin daɗin ma’aikata da ba a warware ba, inda suka yi barazanar tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya.
A cikin wata wasika da Shugaban SSANU, Muhammed Ibrahim ya rattaba wa hannu, ƙungiyoyin sun koka kan rabon kuɗaɗen alawus da suka ce bai yi adalci ba, da rashin biyan wasu hakkokin da ake binta.
Ibrahim ya tuna cewa tun a ranar 18 ga Yuni, 2025, kwamitin haɗin gwiwa na NASU da SSANU ya rubuta wa gwamnati wasika kan batutuwan ƙwadago da ba a warware ba, wanda hakan ya kai ga ganawa da minista a ranar 4 ga Yuli, 2025.
Sai dai a sabon saƙo da aka aika wa rassan ƙungiyoyin a faɗin ƙasar ranar Talata, shugabannin sun ce tsawaita wa’adin ya biyo bayan ganawa da Sakatare na Dindindin na Ma’aikatar Ilimi, Abel Enitan, a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa saboda haka suka tsawaita wa’adin na makonni biyu daga ranar Talata.
Sun ce hakan zai ba gwamnati damar kaddamar da shirye-shiryen warware matsalolin kafin wa’adin ya ƙare.













































