AFCON: Ta bawa NTA damar yada gasar wasanni 52

AFCON logo
AFCON logo

A wata sanarwa da Hukumar Gidan Talabijin ta kasa NTA ta fitar, ta sanar da cewa ta samu damar yada wasanni 52 na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka wato AFCON.

Karanta wannan: Gwamnatin Najeriya ta wofintar da mu a Sudan-Wasu Dalibai

Wata majiya a shafin X, ta bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Laraba tare da Afro Sports.

Inda ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “NTA ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da Afro Sports don yada wasanni 52 na gasar cin kofin Afrika a kasar Cote d’Ivoire.”

Tun da farko, Multichoice, ya bayyana cewa ba za’a yada gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka da za’a yi a dandalinsa ba.

Karanta wannan: ‘Yan sanda sun yi fatali da sace matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Kasancewar an samu tsaikon gazawar tauraron dan adam da zai yada shirye-shiryen wasan kwallon kafa mafi girma a tashoshinsa na SuperSport.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here