‘Yan sanda sun yi fatali da sace matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

police 750x430
police 750x430

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta karyata rahotannin sace mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talata ne wasu  kafafen yada labarai suka rawaito cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kusan 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi.

Karanta wannan: Hukumar ‘yan sanda ta gargadi jami’anta da su guji karbar na goro a wajen masu neman aiki

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, yayin da yake karyata labarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya amince cewa an yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga da suka yi yunkurin tsallaka babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a unguwar Dogon Fili zuwa Jere, a ranar 6 ga watan Janairu, inda wasu daga cikin ‘yan fashin suka tsere da raunukan harsasai.

Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin da ake artabun wasu mutane shida da ke kan hanyar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Karanta wannan: Sheikh Gumi yace da gangan Sojoji suka kai hari kan masu Mauludi a Tudun Biri

Amma ya ce babu wanda ‘yan bindigar suka sace kamar yadda aka yi ta yadawa a wasu kafafen yada labarai.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa da su, da suka hadar da Jibrin Tasiu da Jummai Abubakar da Zafira Abubakar da Abdulkarim Nurudeen da Lance Kofural Chinedu Moneke da Ayo James.

Karanta wannan: Hukumar NUC ta magantu kan Farfesoshin bogi a Jami’o’i

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yammaci da kuma tsakiyar Najeriya da ‘yan bindiga ke addabar kauyuka tare da kashewa da sace mutane baya ga kona gidaje bayan sun yi awon gaba da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here