Shugaban hukumar ‘yan sanda ta kasa Solomon Arase, ya gargadi jami’an hukumar da aka tura domin daukar sabbin ‘yan sanda, da su guji karbar kudade daga wajen masu neman aikin.
Arase, ya yi gargadin ne a wajen taron tantance jami’an da za su yi aikin tantance sabbin ‘yan sandan ranar Asabar, gabanin atisayen da za a fara ranar Litinin a fadin kasar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya fitar ranar Lahadi.
Karanta wannan: Kano: ‘Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya yi wa ‘yar uwarsa ciki kuma ta mutu
A cewar Arase, matukar an gudanar da aikin yadda ya kamata, martabar da kimar hukumar ba zata ragu ba.
Ya ce karbar kudi daga masu neman aikin ko ‘yna uwansu ya saba wa ka’idar aikin kuma cin amana ne.
Ya jaddada cewa jami’an ba wai kawai suna gudanar da aikinsu ba ne, illa dai suna tsara makomar rundunar.
Karanta wannan: Sabon rikici ya barke tsakanin Hukumar ‘Yan Sanda, Babban Sifeton Yan sanda
Shugaban ya umarci jami’an da su bi ka’idojin aikin tare da nuna kwarewa da kuma da’a a duk tsawon lokacin da zasu yi suna gudanar da atisayen.
Shugaban ya yi nuni da cewa daukar ma’aikata na da matukar muhimmanci domin shi ne na farko da hukumar ta gudanar bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 20 ga watan Yulin 2023, wanda ya tabbatar da fifiko ga hukumar wajen daukar aikin rundunar.