Hukumar yaki da sha da fataucin miyaguin kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta cafke kimanin kunshi 66 na wani nau’in tabar wiwi, kunshe kunshe a cikin koren ganyen shayi da aka shigo da su ta filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Ikeja birnin Lagos.
SolaceBase taruwaito cewacafke wadannan miyagun kwacen a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da aka samu gabanin isowar kayan sashen jigilar kayayyaki na filin jirgin a ranar 11 ga Mayu.
Hukumar ta NDLEA ta sanya ido kan jigilar kayayyaki tare da ci gaba da sa ido a kai sama da makonni uku kafin ta gayyaci sauran masu ruwa da tsaki don yin aikin hadin gwiwa a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi a Abuja, ta ce, an boye miyagun kwayoyin ne mai nauyin kilogiram 62 da digo 20 a cikin kwalayen ganyen shayin da aka yo safararsu daga kasar Thailand ta hanyar jirgin hadaddiyar daular Larabawa na Emirates.
A wani samame da aka yi a Legas, jami’an NDLEA a ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, sun kama wani nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,665, a hanyar Lekki zuwa Ajah.
Ba tare da bata lokaci ba an damke wasu mutane biyu Gidado Abdulrasaq Ayinde da Obanla Oluwafemi da hannu wajen safarar su.
A Kaduna, jami’an hukumar NDLEA na jihar da ke sintiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata, 3 ga watan Yuni, sun kama Goodluck Nnaemeka, dan shekara 29, dauke da kwalabe 612 na maganin da ke dauke da Codeine da kuma kwayoyin flunitrazepam guda 2,970.
A wani samame da aka yi a wannan rana, an kama wani mai suna Kabiru Musa mai shekaru 52 da ake nema ruwa a jallo a Kurmin Mashi.
An gano jimillar skunk mai nauyin kilogiram 25 da digo 7 a baya daga sansaninsa.
A yayin da aka kwato jimlar miyagun kwayoyi mai nauyin kilogiram 9 a wata mota kirar Audi mai lamba AAA 975 XU wadda Atari Israel mai shekaru 45 ke tukawa a hanyar garin Auchi na jihar Edo, an kama wasu matasa biyu Favor Joy da Joy Igwe a ranar Talata 3 ga watan Yuni a yankin tudun Ikpoba na birnin Benin.












































