Fasinjoji uku sun rasa rayukansu yayin da jirgin Warri–Itakpe ya yi hatsari a Delta

Warri Itakpe train accident

Fasinja uku sun mutu bayan da jirgin da ke kan layin Warri–Itakpe Train Service ya fita daga kan layin dogo ya yi hatsari.

Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin.

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, Hukumar Kula da Hanyoyin Jirgin Kasa ta Kasa (NRC) ta ce kungiyoyin agajin gaggawa da sauran hukumomi da suka dace yanzu haka suna wurin da lamarin ya faru suna bada agajin da taimakon da ya dace.

Hukumar ta NRC ta tabbatar da cewa hatsarin na Warri–Itakpe Train Service WITS ya auku ne a yau.

“Jami’an bada agajin gaggawa da hukumomin da suka dace yanzu haka suna wurin da lamarin ya faru suna ci gaba da da ba da taimakon da ya dace,” in ji sanarwar da babban darakta Janar Kayode Opeifa ya sanya wa hannu.

“Hukumar na ci gaba da san ya ido kan yadda lamarin yake kuma za a fitar da cikakkiyar sanarwa da zarar an samu karin bayani,” in ji ta.

Hatsarin ya faru ne kasa da wata guda bayan NRC ta dakatar da aikin Warri–Itakpe Train Service WITS na wucin gadi, saboda bukatu na aiki da shawarar masana daga injiniyoyinta.

Ta ce dakatarwar ta wucin gadi ta zama dole ne domin ta iya gudanar da muhimman bincike na aiki da nufin tabbatar da ci gaba da tsaro, aminci, da inganta hidima a wannan hanyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here