HURIWA ta soki nadin da Buhari ya yiwa wan uwargidan sa a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga kuɗi na ƙasa

President Buhari sad sad
President Buhari sad sad

Wasu kongiyuyi masu rajin kare hakkin dan adam a Najeriya, da kuma HURIWA, sun soki nadin da akaiwa Ahmed Halilu, a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga kuɗi na ƙasa NSPMC, wanda  shi din babban yaya ne ga mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari.

HURIWA ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karya alkawarin da ya yi lokacin da za’a raantsar dashi a matsayin shugaban kasa, na ba zai yi son rai ba ya yin gudanar da shugabancin sa.

Halilu, wanda wan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya riƙe kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.

HURIWA ta kara da cewa na din da Buharin ya yi san rai ne kawai ba wani abu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here