Firaministar Burtaniya, Liz Truss, ta nada ‘yar Najeriya, Kemi Badenoch a matsayin mamba a majalisar ministocinta a ranar Talata.
Idan za a tuna Badenoch ta yi yunkurin zama Firaministar Burtaniya a matsayin memba ta Jam’iyyar Conservative kuma ta kai matsayi na biyar a watan Yuli.
Sai dai, a wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na Firaministar Burtaniya, @10DowningStreet, an nada Badenoch a matsayin Sakatariyar Harkokin Kasuwancin Kasa da Kasa kuma Shugaban Hukumar Kasuwanci.
Sanarwar ta kara da cewa, “An nada Kemi Badenoch @KemiBadenoch Sakatariyar Harkokin Ciniki ta Kasa da Kasa kuma Shugabar Hukumar Kasuwanci @TradeGovUK # Reshuffle”
Sauran mambobin majalisar ministocin da za su yi aiki tare da Truss kamar yadda Sarauniya Elizabeth ta II ta amince da su, wanda ke kunshe a cikin wata sanarwa su ne:
Rt Hon Dakta Thérèse Coffey, a matsayin Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya da Kula da harkokin Jama’a.
Haka kuma za ta zama mataimakiyar Firaministar.
Rt Hon James Cleverly, a matsayin Sakataren harkokin Kasashen Waje, sai Rt Hon Suella Braverman QC, a matsayin Sakatariyar Gwamnati ta Ma’aikatar cikin dida, yayin da Wendy Morton ke a matsayin Sakataren Majalisar Dokoki ga Baitulmali (Kuma babban bulalar majalisar), da sauransu.













































