Da Dumi-dumi:Chelsea ta Kori Thomas Tuchel

skynews thomas tuchel chelsea 5890359 750x430 1
skynews thomas tuchel chelsea 5890359 750x430 1

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kori Manajanta Thomas Tuchel, bayan ta sha kashi a hannun Dynamo Zagreb ranar Talata a gasar cin kofin zakarun Turai wasan rukuni na farko.

Sanarwar da Mai horarwar ya fitar a shafinsa na internet da safiyar Laraba ya ce:

“A madadin kowa da kowa a Kungiyar Chelsea FC, ina so na rubuta godiya ga Thomas da ma’aikatansa saboda duk kokarin da suka yi a lokacin da suke tare da kulob din.

Thomas dai ya shiga tarihin kungiyar Chelsea bayan ya lashe gasar zakarun Turai da Super Cup da kuma gasar cin kofin duniya a zamaninsa.

“Yayin mamallakan sabuwar kungiyar suka cika kwanaki 100 da karbar ragamarta, kuma yayin da su ke ci gaba da kokarin ciyar da kungiyar gaba, sabbin masu hannun jarin sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a yi wannan sauyi.

“Ma’aikatan horar da ‘yan wasan Chelsea za su dauki nauyin kula da kungiyar don horo da kuma shirye-shiryen wasanninmu masu zuwa yayin da kungiyar ke shirye-shirye cikin gaggawa don nada sabon koci.

“Babu wani batu da za a sake yi har sai an nada sabon mai horaswa.”

Thomas Tuchel shi ne mai horaswa na karshe a Kungiyar da ya yi rashin nasara kusan sau uku a cikin wasani bakwai na farkon gasar a kakar wasanni ta bana, bayan Mai horsawa José Mourinho a kakar wasanni ta Shekarar 2015 zuwa 16.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here