Kwamitin shirya gasar wasannin makarantun sakandare a Gombe ya fitar da sabon lokacin fara gasar

IMG 20241010 WA0002

Kwamatin shirya gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle dake Gombe ya sanar da sabuwar ranar da za ta fara gasar, wato daga ranar 11 zuwa 16 ga Nuwamba, 2024, wanda za’a gudanar a babban filin wasa na Pantami dake jihar.

Ana sa ran makarantun sakandare sama da 85 daga kananan hukumomi 11 da ke fadin jihar zasu shiga gasar.

Tun da farko an shirya gudanar da taron a ranar 18 zuwa 24 ga Oktoba, 2024, an dage taron ne saboda wani aikin gwamnati da ya shafi ma’aikatar ilimi ta jihar. A shirye-shiryen gasar, an riga an horar da sama da Masu bada horo 65 daga makarantun sakandare daban daban, inda ake sa ran matasa ’yan wasa kusan 3,065 za su halarci wannan gasar ta firamare. inda ‘yan wasa za su yi zango a girls village lokacin gasar, an kammala, kuma ana gudanar da zaman horo a makarantu a duk fadin.
Hon. Ahmad Shu’aibu Gara-Gombe, shugaban kwamitin shirya gasar, ya bukaci shugabannin makarantu, ‘yan wasa, da masu ruwa da tsaki su shirya dalibansu domin wannan gagarumin gasar .

Ya kuma jaddada cewa, duk shirye shiryen gudanar da gasar suna cikin tsari, kuma karin lokacin da aka samu daga gyare gyaren jadawalin zai ba da damar masu daukar nauyin kulla kawancen da za su kara habaka gasar wasannin motsa jiki, wanda kuma za a rika yadawa ta yanar gizo ga masu sauraro a duniya.

Shugaban na Green White Green (GWG) Sports Center Ltd, Hon. Gombe, ya nuna jin dadinsa kan yadda aka daidaita wannan sabuwar ranar tare da masu ruwa da tsaki daga ma’aikatun wasanni da ilimi. Ya kuma jaddada kudirinsa na ganin cewa gasar wasannin guje guje da tsalle tsalle ta tsakanin makarantun gaba da sakandire ta Gombe ta zama abin tunawa, wanda ya zaburar da sauran jihohin kasar nan wajen yin koyi da shi.

Sanarwar sabuwar ranar ta sake farfado da sha’awa a tsakanin makarantun da ke halartar gasar, tare da yin kokarin ba da horo mai zurfi a shirye shiryen gasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here