Fadar shugaban kasa ta ce abu ne mai wuya majalisar dokokin kasar ta yi watsi da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka kan kudirin gyaran dokar zabe saboda biyayyar jam’iyya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, a wata hira da yayi da wani shiri na gidan Talabijin na Channels TV mai suna “Sunday Politics “, ya bayyana cewa mambobin majalisar ‘yan’yan jam’iyyar APC ba za su yi abinda zai sabawa ra’ayin shugaba Buhari a kan daftarin doka mai cike da takaddama ba.
Shugaba Buhari, a makon da ya gabata, ya ki amincewa da kudurin dokar zabe, kwanaki 30 bayan da majalisar ta mika masa a ranar 19 ga watan Nuwamba.
Sai da Shugaba Buhari ya bayyana rashin tsaro, tsadar gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye da kuma take hakkin ‘yan Najeriya na shiga harkokin mulki a matsayin dalilansa na kin amincewa da kudirin.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar kafin su tafi hutu, sun yi barazanar yin watsi da matakin shugaban kasar bayan suj dawo aiki a watan Janairun 2022.
Sai dai Mista Adesina ya yi watsi da yiwuwar ‘yan majalisar na aiwatar da barazanarsu, ganin yadda jam’iyyar APC ke da rinjaye a majalisun biyu.
Ya yi watsi da yiwuwar sake bullowar al’amura inda ‘yan majalisar jam’iyyar suka yi wa shugaban kasa kaca-kaca a kan wasu muhimman batutuwa a lokacin da Bukola Saraki ya jagoranta.
“Kada mu manta cewa majalisar nan ta kasa musamman ta kunshi fiye da 70, kusan kashi 80 cikin 100 na ‘ya’yan jam’iyyar APC kuma ba ku da wata jam’iyya da za ta harba kanta.” A cewar Adesina.
Yace jam’iyyar APC za ta yi amfani da rinjayen da take da shi a Majalisar Dokoki ta kasa kenan don ganin ba’a kawo wa Shugaban Kasa Buhari wata matsala kan wannan kudiri ba.













































