Kimanin fasinjoji 11 ne suka mutu yayin da 10 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.
Hatsarin wanda ya afku a ranar Juma’a 3 ga watan Nuwamba, ya rutsa da wata mota kirar Volvo DAF mai lamba KW 230 SKK.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta fitar ta ce, motar wani mutum mai suna Sule mai shekaru 40 ne ya tuka motar daga karamar hukumar Gada ta Sakkwato.
Kebbi PPRO, Nafiu Abubakar, a cikin sanarwar, ya ce jami’an ‘yan sanda daga reshen Shanga sun halarci wurin da hadarin ya faru domin gudanar da abinda ya dace.