Dalilin da yasa na kai ƙarar PDP Kotu – Lamido

Sule Lamido Jigawa 720x430

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa ya kai ƙarar jam’iyyar People Democratic Party (PDP) a kotu ne domin dawo da hakkinsa na yin takara a wani muƙami na jagoranci a cikin jam’iyyar.

Lamido ya ce wannan ƙara ba wani hari ba ne kan jam’iyya, sai dai gwagwarmaya ce domin kare mutuncinsa da martabarsa da aka tauye masa.

Ya kara da cewa ya garzaya kotu ne domin dawo da abin da jam’iyyar ta hana shi, ba wai saboda wani mutum ko wani abin siyasa ba.

Tsohon gwamnan ya nuna takaici kan yadda jam’iyyar ta lalace, inda soyayya, haɗin kai da amana a tsakanin mambobi suka ragu sosai.

Duk da cewa ya samu nasara a ƙarar, ya ce abin ya ci masa zafi ganin rikicin ya shafi jam’iyya da ‘yan uwansa.

Lamido ya ce ba zai iya janye ƙarar ba saboda kotu ta riga ta yanke hukunci, sannan ba zai halarci taron gangamin jam’iyyar da aka shirya a Ibadan a ranar 15 ga Nuwamba ba.

Ya ce halarta taron da kotu ta hana gudanarwa zai yi daidai da watsar da abin da ya samu daga hukuncin kotu.

Ya kara da cewa, kotu ta dawo masa da mutunci, don haka zai tsaya kan hukuncin kotu domin bin doka da oda.

Lamido ya kuma zargi wasu gwamnonin jam’iyyar da lalata tsarin PDP, inda ya bayyana cewa daga gwamnonin 14 na baya yanzu suka rage uku, wanda hakan ya nuna matsalolin cikin gida.

A baya Lamido ya shigar da ƙara saboda an hana shi damar sayen takardar tsayawa takara don zama shugaban jam’iyyar a taron gangamin, kuma kotun tarayya ta haramtawa PDP gudanar da taron har sai an warware ƙarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here