Rundunar sojin Najeriya ta musanta sace kwamandan rundunar a jihar Borno

nigerian army training

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da suka bayyana cewa an sace kwamandan rundunar aiki na musamman ta 25, Birgediya Janar M. Uba, lokacin wani kwanton bauna da ’yan ta’adda suka yi a yankin Wajiroko, Azir-Multe na karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

A cewar rundunar, wannan bayanin ya fito ne daga wata sanarwa da mataimakiyar Daraktar hulɗa da jama’a ta rundunar soji, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta fitar a Maiduguri ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun rundunar suna gudanar da sintiri na yau da kullum domin tabbatar da tsaron al’ummomi a yankin Wajiroko da gefen dajin Sambisa.

Rundunar ta ce yayin dawowar dakarun zuwa sansani ne suka gamu da matsanancin harin ’yan ta’adda.

Ta kuma tabbatar cewa dakarun sun amsa harin tare da ci gaba da aikin tsaro a yankin.

Rundunar sojin ta ƙara da cewa babu wani lamari na sace kwamandan ko wani babban jami’in rundunar a wannan tashin hankali, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da kare al’umma da kuma tabbatar da tsaro a dukkan yankunan da take aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here