Cibiyar kare hakkin dan adam da tabbatar da adalci a ayyukan gwamnati ta (CISLAC) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) da hukumar leken asiri ta kasafin Kudi (NFIU) suna gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba.
Babban Darakta na CISLAC, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani) ne ya bada shawarar, bayan fitar rahoton Transparency International (TI) na shekarar 2024 na cin hanci da rashawa (CPI) a Abuja.
Cibiyar ta jaddada bukatar samar da isassun kudade da tallafi ga wadannan hukumomi domin yakar cin hanci da rashawa yadda ya kamata.
Labari: Kungiyar CISLAC ta nuna damuwa kan karin kasafin kudi na Naira tiriliyan 54.2
Musa ya zayyana matakai da dama don inganta tsarin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ciki har da yin gaggawar yin shari’a kan shari’ar cin hanci da rashawa.
Sa ido kan mutuncin shari’a, gami da hanyoyin ba da labari da bayyana kadara.
Ya ce, “Bincike na rashin son kai game da cin hanci da rashawa a bangaren tsaro ya zama dole don magance matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar nan, da tsauraran dokar sayan kayayyakin gwamnati na shekarar 2007, tare da yin cikakken bincike da yadda jama’a ke samun kwangila da kasafin kudin gwamnati.