Rundunar sojin Najeriya ta tura dakarun wanzar da zaman Lafiya 173 Guinea Bissau

Nigeria Army
Nigeria Army

Rundunar Sojojin Najeriya ta tura dakarunta 173 zuwa kasar Guinea Bissau, domin aikin wanzar da zaman lafiya na kungiyar ECOWAS, a wani bangare na karfafawa da inganta tsaro a yankin yammacin Afirka.

Babban jami’in gudanarwa na hedikwatar rundunar, Manjo Janar Oluwafemi Akinjobi, shi ne ya sanar da hakan ranar Alhamis yayin bikin yaye sojoji daga cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai da ke Jaji Kaduna.

Taron yaye daliban na zuwa ne gabanin tashinsu zuwa Bissau, babban birnin kasar Guinea Bissau yayin da ake sa ran za su bar Najeriya nan take.

Da yake jawabi ga sojojin, babban hafsan rundunar wanda Manjo Janar Zakari Abubakar ya wakilta, ya gargadi rundunar da su bi ka’idojin aiki, da nuna jarumtaka a matsayinsu na kwararru, da kuma mutunta al’adun mutanen Guinea Bissau.

“Najeriya ta kasance matattarar zaman lafiya kuma mai tsaron yankin ECOWAS.

Don haka gwamnatin Najeriya ta himmatu wajen tura tawagar wanzar da zaman lafiya zuwa jamhuriyar Guinea Bissau,” inji shi.

“Tarihin wanzar da zaman lafiya a Afirka ba zai cika ba sai an sanya sadaukarwar da Nijeriya ta yi.

Tawagar farko ta dakarun wanzar da zaman lafiya a Najeriya an tura su ne a shekarar 1960 jim kadan bayan samun ‘yancin kai.

“Tun daga wancan lokacin, Najeriya ta ci gaba da bada gudummawar sojoji sama da 100,000 a ayyukan wanzar da zaman lafiya sama da sau 40 a Afirka da ma duniya baki daya.

Dole ne na fada da alfahari cewa dakarun wanzar da zaman lafiya sun dawo da zaman lafiya a yankuna da dama da ake fama da rikici a duniya wanda ya sa Najeriya ta samu yabo da yawa a fadin duniya.”

Abubakar ya tunatar da sojojin cewa Majalisar Dinkin Duniya ba ta jurewa safarar miyagun kwayoyi da take hakkin dan Adam.

Ya kuma bukace su da su guji munanan halaye masu iya bata sunan sojojin Najeriya da ma kasar baki daya.

A nasa jawabin, kwamandan cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai, Manjo Janar Auwal Fagge, ya bayyana muhimmancin bayar da horon kafin a tura sojoji.

Ya ce horon ya yi daidai da muradin hedikwatar sojojin Najeriya na tabbatar da cewa sojojin sun samu horon da ya kamata kafin shigar da su ayyukan wanzar da zaman lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here