Zaben 2023: Farfesoshi sun marawa Osinbajo baya

Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi kira ga malaman jami’o’i da sauran kwararru da su fito su taka rawa wajen ganin Najeriya ta zama kasa mafi kyau ga kowa.

A wata sanarwa da Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, ya fitar ranar Alhamis a Abuja, ya ce mataimakin shugaban kasar ya karbi, a ziyarar ban girma daga wata tawagar farfesoshi 13 da suka zo don nuna goyon bayansu ga muradinsa na tunkarar zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Manyan malaman jami’o’in wadanda suka fito daga shiyyoyin Najeriya shida, sun ziyarci Osinbajo ne karkashin inuwa guda.

Kungiyar ta samu jagorancin Farfesa Shehu Adamu, shugaban tsangayar nazarin kiwon lafiya na jami’ar karatu daga gida ta Najeriya NOUN.

Mataimakin shugaban kasar ya tuna da kwarewarsa a matsayinsa na malami wanda ya zama babban lauya.

Osinbajo ya yi maraba da goyon bayan da malaman suka nuna na zabensa a zaben shugaban kasa na shekarar 2023 mai zuwa.

Ya kuma yaba da yadda kungiyar ta amince da kudirin sa na neman shugabancin kasa.

Ya ce idan har akwai wata amincewa da ta ba shi farin ciki na musamman, amincewar kungiyar ce.

Tun da farko a nasa jawabin, Jagoran tawagar Farfesa Shehu Adamu ya ce sun kai ziyarar ne domin ganawa da mataimakin shugaban kasa kan ayyuka da kokarin kungiyar na mara masa baya kan burinsa na zama shugaban Najeriya.

Ya ce malaman jami’o’in sun gamsu da kwarin gwiwar da Osinbajo ke da shi na shugabancin Najeriya, don haka sun kuduri aniyar ci gaba da bashi gudunmawa don ganin ya yi nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here